21 Afirilu 2021 - 12:44
Najeriya: Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Ya Amsa Tambayoyi A Hannun EFCC

A jiya Talata ce jami’an tsaro a hukumar EFCC mai yaki da cin hinci da kuma yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annuti suka tsare tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul Aziz Yari nan sa’o’i masu yawa, inda yake amsa tambayoyi dangane da cin hanci da rashwa a gwamnatinsa.

ABNA24 : Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa tun ranar 6 ga watan Afrilun da muke ciki ne hukumar ta EFCC ta mikawa tsohon gwamnan wasikar gayyata zuwa ofishinta da ke birnin Sokoto a ranar 8 ga watan Afrilun da muke ciki, amma Yari bai amsa gayyatar ba sai a jiya Talata 20 ga wata.

Labarin ya kara da cewa tsohon gwamnan ya isa ofishin hukumar ne da misalin karfe 11 na safe kuma har zuwa karfe 7 na yamma ya na tare da jami’an hukumar. Har’ila yau na ce ya zuwa lokacin hada wannan rahoton an bada belinsa amma bai cika sharuddan karban belin ba.

A cikin watan Fabrairu da ya gabata ma, tsohon gwamnanan ya sha tambayoyi a ofishin hukumar ta EFCC da ke birnin Lagos kan kokarin yin sama da fadi da wasu kudade kimani naira biliyon 300 da ke cikin wani asusu a bankin Generation Bank a birnin na Lagos.

342/